A cewar kamfanin dillancin labarai na AFP, dubban mutane sun nemi mafaka, an rufe tashoshin jiragen ruwa sannan zaftarewar kasa ta rufe hanyoyi a yankuna masu tsaunuka a kasar ta Philipines a yau Litinin, a yayin da guguwa ta sake afkawa kasar da iftila’i a karo na 4 a kasa ta wata guda.
Guguwar Toraji mai dauke da ruwan sama ta afka kusa da garin Dilasag, mai tazarar kimanin kilomita 220 daga arewa maso gabashin babban birnin kasar, Manila, da safiyar yau, a cewar hukumar kula da yanayin kasar.
“Iska mai karfi da mamakon ruwan sama ne suka afka mana. Wasu bishiyoyi sun fadi kuma lantarki ya katse tun jiya,” kamar yadda shugaban hukumar tsaron farin kaya ta garin Dinalungan dake kusa da Dilasag, Merwina Pableo, ya shaidawa AFP.
Har yanzu ba’a samu asarar rai ba sa’o’i 11 bayan da guguwar ta ratsa tsakiyar tsibirin Luzon mai yawan tsaunuka, kamar yadda masu aikin ceto a lardin suka shaidawa AFP.
Sun bayyana cewa an kwashe akalla mutane 8, 000 daga yankunan bakin teku da wadanda ake ganin za’a iya samun ambaliyar ruwa ko zaftarewar kasa a lardunan Aurora da Isabela da Ifugao da wurare masu tsaunuka.
Gabadaya, gwamnatin ta bada umarnin kwashe jama’a daga kauyuka 2, 500 a jiya Lahadi, duk da cewar hukumar kula da bala’o’i ta kasar bata bayyana jumlar mutanen da aka kwashe din ba zuwa yau Litinin.