Wani babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya, ya ce, Majalisar ta saka kokon neman taimakon dala miliyan dari-biyu-da-tamanin-da-biyu, domin a tallafawa wadanda bala’in guguwar Idai ta shafa a Mozambique.
A jiya Litinin Mark Lowcock ya ce, za a yi amfani da kudaden wajen samar da ruwan sha, magunguna da tsabtace muhalli, da samar da abinci da kuma taimakawa al’umar da bala’in ya shafa domin su koma bakin sana’o’insu.
Guguwar ta Idai, ta halaka akalla mutum 750 a Mozambique da Malawi da kuma Zimbabwe da ke makwabtaka da juna, sannan ta raba dubban daruruwan mutane da muhallansu.
Ita gamayyar kungiyoyin ba da agajin gaggawa ta Red Cross da Red Crescent, ta nemi taimakaon dala miliyan talatin-da dugo-biyar, domin a samar da kayayyakin agaji ga mutum dubu 200 da suka fi galabaita sanadiyar wannan guguwa.
Sakatare Janar na gamayyar kungiyoyin, Elhadi As Sy, ya nuna bukatar samar da wadannan kudade, bayan wata ziyarar da ya kai wani sansanin da mutane suka fake.Ya ce, “Daya daga cikin inda na ziyarta makaranta ce, tana dauke da mutum dubu uku, kuma azuzuwa sha biyar ne kacal a makarantar, ban daki shida, sannan ita kanta makarantar, ambaliyar ruwa ta mamaye wani sashinta.”
Facebook Forum