An Sassauto Da Dokar Hana Fita A Jihar Yobe

Kakakin soja Kyaftin Eli Lazarus, yace a yanzu an mayarda dokar hana fita waje ta koma daga karfe 4 na yamma zuwa 7 na safiya
Bataliyar zaratan sojojin runduna ta 3 ta Najeriya ta sassauto da dokar hana fita waje da ta kafa a fadin jihar Yobe a bayan wani farmakin da 'yan bindigar kungiyar Boko Haram suka kai kan Damaturu, babban birnin jihar a ranar alhamis da daddare.

A cikin wata sanarwar da ya aikewa da 'yan jarida ta sakonnin Text, kakakin bataliyar sojojin dake yakar 'yan bindiga a Yobe, Kyaftin Eli Lazarus, yace a yanzu dokar hana fitar zata fara aiki ne daga karfe 4 na la'asar zuwa karfe 7 na safiya.

Tun da farko dai a jiya jumma'a, Kyaftin Lazarus ya bayar da sanarwar kafa dokar hana fita waje baki daya a deuk fadin jihar a yayin da rundunar take farautar 'yan bindigar da nufin hana su sake sulalewa.

Rundunar ta kuma yi kira ga jama'a masu bin doka da oda da su ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum kamar yadda suka saba daga karfe 7 na safiya har zuwa karfe 4 na la'asar.