An Samu Saukin Rashin Tsaro Tunda Aka Fara Kutsawa Daji Ana Kashe ‘Yan Bindiga: El-Rufai

Gwamnan Kaduna Malam Nasiru El Rufai (Facebook/El Rufai)

Gwamna Nasiru Ahmed El-rufa'i na Jihar Kaduna ya ce shawarar da su ka dade su na baiwa gwamnatin tarayya ta kutsawa daji don kashe 'yan-bindiga, wadda sai yanzu gwamnati ta fara aiki da ita, yanzu cikin takaitaccen lokaci matsalar tsaro ta yi sauki.

KADUNA, NIGERIA - Gwamna Nasiru Ahmed El-rufa'i wanda ke jawabi ga kungiyar 'yan-kasuwa jiya Alhamis a gidan gwamnati, ya ce indai jami'an tsaro za su ci gaba da shiga daji don farautar 'yan-bindiga to kwananan za a kawo karshen matsalar tsaro.

‘Yan Bindiga

El-rufa'i ya ce tun da mutuwa dole ce, to idan jami'an tsaro sun shiga daji, duk wanda su ka samu kawai su kashe koda kuwa shine a hannun 'yan-bindigan.

Ya ce yanzu hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari da Kaduna zuwa Abuja da kuma wasu yankunan Jihar Kaduna duk an sami saukin matsalolin tsaro saboda mutane za su iya ci gaba da harkokin su na yau da kullun.

Yanzu dai jami'an tsaro sun fatattalki 'yan-bindigan daji har da na wasu yankunan Jihar Kaduna kuma masana kan harkokin tsaro irin su Manjo Yahaya Shinko mai ritaya sun ce aikin jami'an tsaron abun a yaba ne duk da dai yana da alaka da gangarowar zabe.

Manyan sojojin Najeriya (Facebook/Fadar shugaban kasa)

Manjo Shinko ya ce duk da yake kowa zai yi murnar murkushe matsalar tsaro amma duk aikin jami'an tsaron ya zo dab da lokacin cire takunkumin yakin neman zaben shugaban kasa, to dole ne a alakanta aikin da siyasa.

Wannan dai ba shine karon farko da gwamnan Jihar Kaduna ke kira ga jami'an tsaro da su kutsa daji neman 'yan-bindiga ba sai dai wannan ne na farko da ya nuna gamsuwa da matakin jami'an tsaron da ya ce zai kawo karshen matsalar tsaro.

Saurari rahoton Isah Lawal Ikara:

Your browser doesn’t support HTML5

An Samu Saukin Rashin Tsaro Tunda Ake Kutsawa Cikin Daji Kashe ‘Yan Bindiga: El-Rufai.mp3