Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mafarauta Sun Kashe ‘Yan Bindiga Sama Da 20 A Jihar Taraba


.
.

Kungiyar mafarauta ta hadin gwiwa ta kashe ‘yan bindiga sama da shirin a dajin yankin Bali da Gossol a Jihar taraba, sun kuma tarwasta sansanin ‘yan bindigan da suka hana mazauna yankin zaman lafiya. 

TARABA, NIGERIA - A ci gaba da kokarin samar da zaman lafiya Kwamandan da ya jagoranci artabun hadin gwiwa da ya hada da ‘yan banga, ya ce sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga sama da ashirin, kuma yanzu haka suna kan samun nasarar akan ‘yan bindiga.

Malan Zakari Yanli, daya daga cikin ‘yan banga kuma mai kishin Jihar, da al’ummarsa ya tabbatar da cewa ba za su bar wannan yakin ba har sai an kawo karshen mastalar rashin tsaro a jihar baki daya.

A nasu bangaren, Al’ummomi mazauna yankin sun nuna farin cikin su dangane da yadda ‘yan banga suka taimaka a kokarin dawo musu da yankin su cikin kwanciyar hankali.

Abdullasalam Gambo Mubarak, dan majalisa mai wakiltan Bali da Gossol a Majalisar Wakilan Najeriya, ya tabbatar da faruwar wannan lamari, ya kuma nuna cewa samun ‘yan sa kai zai taimaka sosai wajen kawo karshen mastalar rushin tsaron da ake fama da shi a wannan yankin dama Jihar Taraba gaba daya.

Saurari rahoto cikin sauti daga Lado Salisu Muhammad Garba:

Wasun’Yan Kungiyar Mafarauta Sun Kashe ‘Yan Bindiga Sama Da ishirin A Jihar Taraba.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG