An samu baraka a jam'iyyar UDR a zaben zagaye na biyu a Nijar

Hamma Ahmadu shugaban MODEN Lumana da jam'iyyun hamayya suka tsayar

Daya daga cikin jam'iyyun hamayya da suka ce sun tsayar da Hamma Ahmadu a matsayin dan takararsu a zaben shugabankasar Jamhuriyar Nijar ta ce ba da yawunta aka cimma matsaya ba akan Hamma ba.

Rabuwar kawunan a tsakanin 'yan jam'iyyar ta UDR ta biyo bayan sanarwar da jam'iyyun kawancen adawa ya bayar a karshen mako inda suka bayyana goyon bayansu ga Hamma Ahmadu na MODEN Lumana da zai fafata da shugaban kasar na yanzu Mahammadou Issoufou.

Kusoshin jam'iyyar UDR a jihar Tawa a karkashin jagorancin Mahamud Sadun sun ce basu amince da matsayin shugabansu Ahmadu Bubakar Sise ba. Sun ce su a Tawa basa goyon bayan Hamma Ahmadou. Mahammadou Issoufou ne zasu jefa wa kuri'unsu. Suna cewa kamata ya yi kafin a dauki wani mataki an zanna dasu an yi shawara amma ba'a yi hakan ba.

Amma wata mambar kwamitin kolin UDR Hajiya Rabi Arzika ta bayyana cewa basu taba yadda da ra'ayin 'yan reshen Tawa ba. Dama basu zauna cikin jam'iyyar ba har a yadda dasu. Inji Hajiya Rabi mutanen 'yan rahoto ne. Tace zasu goya ma Hamma Ahmadu baya domin shirinsa ya fi kusa da nasu.

Bangarorin da zasu shiga zagaye na biyu tuni suka fara kama kafafuwan 'yan siyasa da magoya bayansu.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

An samu baraka a jam'iyyar UDR Tabbata a zaben zagaye na biyu a Nijar - 2' 31"