An Sako Mahaifin Dan Wasan Liverpool Da Aka Yi Garkuwa Da Shi

Mahaifin Luiz Diaz da aka sako

An sako mahaifin Diaz ne a bayan da ya kwashe kwanaki 12 bayan da aka sace shi a wani gari da ake kira Barrancas

Gwamnatin Colombia ta sanar da sako mahaifin dan wasan Liverpool Luis Diaz wanda wata kungiyar guerrilla mai ta da kayar baya ta yi garkuwa da shi.

An sako mahaifin Diaz ne a bayan da ya kwashe kwanaki 12.

A ranar 28 ga watan Oktoba aka kama Luiz Manuel Diaz a karamin Barrancas, lamarin da ya janyo hankalin duniya.

Kungiyar masu ta da kayar bayan ta National Liberation Army ko ELN a takaice, ta tabbatar da cewa mambobinta ne suka kama mahaifin Diaz.

Amma sun ce a bisa kuskure ne.

Wata tawagar gwamnati ce ta sanar da sako mahaifin Diaz, wacce ke kan tattaunawa da kungiyar ta ELN kan yadda za a samar da zaman lafiya.