A jiya Lahadi ne aka yi bukin bude hanyoyin wanda gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima da babban hafsan sojan ‘kasa na Najeriya, Tukur Buratai, suka jagoranci bukin bude hanyar da ta tsahi daga garin Maiduguri da Monguno zuwa Baga, da kuma daga Maiduguri da Gubio zuwa Damasak dake karamar hukumar Mobar.
Wannan shine karo na uku da babban hafsan sojan ke bude hanyoyi don baiwa jama’a damar ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum bayan rufe hanyoyin da rundunar sojan suka yi, don samun damar fatattakar ‘yan kungiyar Boko Haram akan hanyoyin.
Yanzu haka dai rundunar sojan Najeriya na ci gaba da bayyana cewa ta kawo karshen maharan ‘yan Boko Haram, inda tace yanzu haka ta fatattakesu a sansaninsu na karshe dake dajin Sambisa.
A cewar janal Buratai, sun kori ‘yan Boko Haram daga dajin Sambisa kuma dajin zai zamanto wani waje na horas da jami’an soja da kuma gwajin makamai a cikin shekara mai zuwa. Daga karshe kuma ya gargadi jami’an sojan da cewa su guji duk wani abin da zai kawo cin hanci gurin masu tafiya akan hanyoyin, kuma duk wanda aka kama za a hukunta shi.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Haruna Dauda.
Your browser doesn’t support HTML5