Daga dukkan alamu babu saura wani wuri dake zama sansanin ‘yan kungiyar Boko Haram, a yanzu, domin dakarun Sojojin Najeriya, a yanzu haka suke rike da dajin Sambisa, kamar yadda Birgediya Sani Usman Kuka Sheka, ya furta.
Yace aikin da rundunar ta tasa a gaba ta sami nasara akai kamar yadda aka baiwa rundunar umarni.
Sudai mayakan Boko Haram, sun binne boma bomai, a cikin dajin Sambisa, domin hanna dakarun tarayya kaiwa garesu, amma tare da taimakon manya mayan tankokin yaki na zamani masu gano inda aka binne boma bomai, Sojojin sun gano tare de kwan kwance wadannan boma bomai, da suka kai ga kwato dajin na Sambisa.
Masana tsaro na alakanta wanna babbar nasara ga kwarewa da kuma jajircewar babban hafsan Sojojin Najeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai, da kuma yada dakarun saman Najeriya, suka yi ruwan boma bomai ta sama a dajin na Sambisa.
Wata majiya mai tushe a hedkwatan Sojan Najeriya, tace sai da dakarun Najeriya suka yi kofar rago a duk sassan dake shiga ko fita daga dajin na Sambisa, kafin su fara lugudan wuta na ayita ta kare.