Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Ginin Ma’aikatar ‘Yan Sanda Ya Ruguje A Birnin Lagos


Rugujewar Ginin Ma'aikatar Yan Sanda A Birnin Lagos
Rugujewar Ginin Ma'aikatar Yan Sanda A Birnin Lagos

A kalla mutane biyu ne suka rasa rayukansu biyo bayan rugujewar wani ginin ma’aikatar ‘yan sanda a yankin Ikeja dake tsakiyar birnin Lagos.

Rahotanni daga rundunar ‘yan sandan jahar Lagos na cewa mutanen sun rasa rayukansu ne sakamakon rushewar ginin, wanda kuma ya kamata a rushe ginin tun a shekara ta 2014, amma kuma aka bar mutanen ke zaune cikin sa ba tare da an tashe su ba.

A cewar kwamishinan ‘yan sandan jahar Lagos, Fatai Owoseni, tuni ya bayar da umarnin a rushe wannan gini tare da sauyawa mutanen dake zaune a ginin matsugunni.

Rugujewar Ginin Ma'aikatar Yan Sanda A Birnin Lagos
Rugujewar Ginin Ma'aikatar Yan Sanda A Birnin Lagos

Rushewar gine gine a Najeriya ba wani sabon abu bane, domin a baya-bayannan ma wata Majami’a ta rushe a yankin Kudi maso Kudancin Najeriya, inda ya kashe mutanen da dama, a jahar Lagos dai an sha samun rahotannin rugujewar gine-gine al’amarin da yake haifar da mutuwar bil Adama.

Domin karin bayani saurari rahotan Babangida Jibrin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:10 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG