Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Matan Chibok Sun Koma Gida Su Yi Bikin Kirsimeti


Wasu daga cikin 'yan mata Chibok 21 da aka kubutar yayin ganawarsu da mataimakin shugaban Najeriya, Prof. Yemi Osinbaji a watan Oktoba
Wasu daga cikin 'yan mata Chibok 21 da aka kubutar yayin ganawarsu da mataimakin shugaban Najeriya, Prof. Yemi Osinbaji a watan Oktoba

Rahotanni daga Najeriya na cewa 'yan matan Chibok 21 da aka kubutar a watan Oktoban da ya gabata sun isa birnin Yola domin komawa gidajensu su gudanar da bukuwan kirsimeti da za a fara a gobe a Lahadi.

Gabanin isarsu, mai taimakawa shugaban Najeriya kan harkar yada labarai Malam Garba Shehu, ya tabbatar da hakan a shafinsa na Tweeter.

Shafin ya ce hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS ta kai 'yan matan su 21 birnin Yola na jihar Adamawa domin su je su yi kirsimeti tare da iyalansu, @GarShehu.

Wakilin Muryar Amurka, Ibrahim Abdulaziz ya ga saukar 'yan matan a lokacin da su ka isa Yola.

Ya kuma ruwaito cewa wannan shi ne karon farko da 'yan matan za su koma gidajensu tun bayan da aka kubutar da su a watan na Oktoba daga hanun mayakan Boko Haram.

Saurari cikakken rahoton domin jin karin bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:55 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG