ACCRA, GHANA - Ruwan sama da aka yi kamar da bakin kwarya na baya-bayan nan da ya dinga zuba a duk fadin kasar Ghana da kuma bude kofofin madatsar ruwa ta Bagre da ke Burkina Faso, sun haifar da mummunar ambaliyar ruwa da ya sa aka rufe makarantu da asibitoci.
An rufe makarantu da asibitocin ne a yankin Tetegu da ke karamar hukumar Ga ta Kudu, inda hukumar ba da agajin gaggawa tare da rundunar soja ne suka dinga taimakawa jama’ar wannan garin.
Wannan shi ne karo na farko da irin wannan ambaliyar ta taba faruwa kamar yadda mutanen da abin ya shafa suka bayyana a lokacin da sSke kirga asarar da suka yi.
Yayin zantawa da daya daga cikin wadanda abin ya shafa ta ce “ni da ‘ya’ya na za mu tafi wurin 'yar uwata da ke Kasoa domin neman agaji, kayan abincinmu, sutura, komai namu ambaliyar ta dauke ta tafi da su.”
Mallam Ibrahim Bossu Sarkin zangon Tetegu daya daga cikin anguwar da ambaliyar ruwar ya rusa da su, ya ce kowace shekara hukumar kula da madatsar ruwar ta kan sanar da su kafin bude kofofin madatsar ruwar Weija.
Stanley Martey Daraktan kula da huldar jama’a ya ce ba batun sanarwa bane, ko da kuwa mun sanar da jama’a ina ruwan zai gudana, duk hanyoyin ruwan jama’a sunyi gini akai, kuma dole a dora alhakin a wiyar shugabannin gundumomin, saboda a halin da ake ciki muna gudanar da bincike kan yadda lamarin yayi muni.
Daraktan NADMO na karamar hukumar Ga ta Kudu, Christian Afiadyo, ya ce sama da mutane 1500 ne suka rasa matsugunansu, kuma har yanzu hukumar tana kai kayan taimako ga wadanda abin ya rutsa dasu.
Saurari cikakken rahoto daga Hawawu Abdul Karim:
Your browser doesn’t support HTML5