An Rantsar da Joe Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46

An rantsar da Dan Jam’iyyar Democrat Joe Biden, a yau Laraba a matsayin shugaban Amurka na 46 a Majalisar Amurka.

Biden, mai shekaru 78, ya zama shugaban kasar mafi tsufa, wanda ya kwashe shekaru 36 a matsayin dan majalisar dattawan Amurka, kuma ya shafe shekaru 8 a matsayin mataimakin shugaban Amurka. Biden ya shafe kusan rabin karni a Washington.

Biden ya yi rantsuwar shiga ofishin shugaban Amurka, inda ya tabbatar da bin Kundin Tsarin Mulkin Amurka da kuma kare kasar daga dukkan makiya, na kasashen waje da na cikin gida.

Mataimakiyar Shugaban Amurka

Jim kadan kafin haka, aka rantsar da Kamala Harris, tsohowar ‘yar majalisar dattawan Amurka daga Carlifornia, jihar da ta fi yawan jama’a, a matsayin mataimakiyar shugaban Amurka. Ta kuma zama mace ta farko bakar fata kuma jinsin Indiya ta farko da ta rike mukami mafi girma a cikin sama da karni biyu na tarihin Amurka.

tutocin da aka jera a dandalin rantsar da shugaban kasa

A jawabinsa na farko, Biden ya ce "Mun ji bukatun mutane, kuma mun saurari bukatun mutane. Mun sani cewa, damokiradiyya na da daraja, kuma dimokiradiyya na da rauni. Amma a wannan lokaci, abokaina, dimokradiyya ta yi nasara.”

Ya kara da cewa, “Wannan ita ce ranar Amurka. Wannan rana ce ta dimokiradiyya. Rana ce a cikin tarihi na launin fata, na sabuntawa da warwarewa.” Biden ya kara da cewa, "hadin kai shi ne tafarkin ci gaba."

tarihin-rantsar-da-shugaban-kasa-a-amurka

muna-so-biden-ya-maida-hankali-kantattalin-arzikin-afrika---boube-namaiwa

Bikin rantsuwar ya samu halartar tsoffin shugabannin Amurka guda uku - Barack Obama, George W. Bush da Bill Clinton - amma shugaban mai barin gado na kasar, tsohon shugaban Amurka Donald Trump, ya yi biris da al'adun shekaru 152 na shugabannin da ke halartar rantsar da magajinsu. Inda ya bar Washington zuwa gidansa na gabar tekun Atlantika a jihar Florida a daidai lokacin da ake bukin rantsar da magajinsa.

trump-ya-kammala-wa-adin-mulkinsa

amurka-dawowar-yan-dimokarat-kan-mulki-bayan-shekaru-hudu