An Rage Tsawon Wa'adin Dokar Hana Fita a Maiduguri

  • Ibrahim Garba

Wasu daga cikin dinbin gawarwakin wadanda su ka mutu a tashin hankalin.

Hukumomi a jihar Borno na arewa maso gabashin Nijeriya sun rage dokar hana fita kuma tuni ma aka maido da sadarwar waya a wasu wurare ne jiahr.
Gwamnatin jihar Borno da hukumomin tsaro daban daban a jihar sun fidda sanarwar hadin gwiwa ta rage dokar hana fita daga sa'o'i 24 zuwa sa'o'i 11. Wato za a rinka fita daga karfe 7 na safe zuwa karfe 6 na yamma.

Idan an tuna dai tun daga ranar Litini da ta gabata aka kafa wannan dokar ta hana fita bayan da wasu 'yan bindigar da ake kautata zaton 'yan kungiyar nan ce ta Jama'atu Ahlissunnah Lid Daawati wal Jihad, wadda ake wa lakabi da Boko Haram. To amma dokar ba ta shafi ma'aikatan asibiti da 'yan kwana-kwana da 'yan jarida da sauran wadanda aka fai bukatar ayyukansu a yanayi irin wannan.

Wakilinmu a jihar ta Borno, Haruna Dauda Biu, ya ce wasu mutanen da su ka fito sabanin dokar sun sha bulala da kuma tsallen kwado. Haruna Dauda ya kuma ce Gwamnan jihar ta Borno Hon Kashim Shatima bai wa 'yan hijar hakuri saboda mawuyacin halin da aka fada. Amma, in ji Haruna, tuni ma wayoyin tafi da gidanka su ka fara aiki a wasu sassan birnin Maiduguri.

Your browser doesn’t support HTML5

An Rage Dokar Hana Fita A Borno


.