Sabili da zuwan shugaban kasa Goodluck Jonathan hukumomi sun tsaurara matakan tsaro a Gombe da kewaye domin ya bude taron tattalin arziki na shiyar arewa maso gabas. To saidai shugaban kare hakin dan adam a jihar Gombe Ibrahim Garba Wala ya ce jami'an tsaro sun kama daruruwan matasa ba tare da samunsu da wani laifi ba.
Ya ce an san al'ada ce idan wani shugaban kasa zai zo a yi kokarin kebe wani wuri ko abu na kunya wanda za'a nuna gazawa na a tattara matasa da ake ganinsu wani abun kunya. Ya ce irin wannan aiki ne kawai na ganin ido. Amma abun takaici, me ya sa ba'a kama yaran ba sai yanzu da shugaban kasa zai zo. Akwai dakin kulle mutane a caji ofis na 'yansanda da yara sun kai hamsin da aka kama suna ciki.Ya ce ya ga 'yanuwa da ya sani da ma wasu idon sani. Mutane da dama suna neman a fida masu 'ya'yansu.
Wani mutum mai suna Ado Mai Nama ya ce shi ma an kama danuwansa. Ya ce bayan ya yi sallar magaruba ya tura yaron ya kawo masa shayi, Tsakaninsa da yaron titi ne ya rabasu amma sai ya ji yaron ya kwala masa kara yana cewa jami'an tsaro sun kamashi domin shugaban kasa zai zo. Ya ce ya nemi belinsa amma aka fada masa sai bayan shugaban kasa ya zo ya kuma koma lafiya sai duk mai neman beli ya je ya nema.
To sai dai kakakin 'yan sandan jihar Gombe DSP Attajiri ya ce duk wanda ya ce an kama wani ba tare da ya yi wani laifi ba to karya ya keyi.
Ga Abdulhwahab Mohammed da rahoto.