Anji daga bakin majiyar labarai na shaidawa wakilin muryar Amurka cewa an kai harin na goshin Magharibar Litinin ne, kan wasu kebabbun wurare dake zagayen filin sauka da tashin jiragen saman birnin Maiduguri, ciki harda cibiyar mayakan jiragen saman Nigeria.
Soja sun killace duk hanyoyin dake kaiwa filin jirgin saman bayan da aka kai harin. Anji wani jami’in Gwamnatin jihar Borno yana shaidawa wakilin muryar Amurka cewar jami’an soja na gudanar da bincike domin kokarta gano makamashin harbawa da tada boma-boman. Ana kuma ci gaba da farautar ‘yan tsagerar.
Rundunar sojin Nigeria ta fidda sanarwar dake cewa ta sami nasarar kora da hana samun nasarar hare-haren da ‘yan Boko Haram ke shirin kaiwa bayan sun sami sukunin satar shiga wasu sassan da Kewayen Maiduguri.’Yan tsagear sun kuma jikkata sosai. Sanarwar tace yanzu dai al’amura sun fara daidaituwa a zagayen filin jirgin saman da kuma Kauyen Jantilo dake kusa. Ana kuma yin kira ga mazauna yankunan da abin ya shafa da su girmama dokar hana yawon, domin baiwa jami’an tsaro sukunin bin sawun ‘yan ta’addar.Wannan dai shine karo na farko da hukumomin jihar Borno suka kafa dokar hana yawo a Maiduguri tun shekarar 2009.
Jihar Borno na daya daga cikin jihohi ukun dake Arewa maso gabashin Nigeria da shugaba Goodluck Jonathan ya kafawa dokar ta baci a watan Mayun a zaman wani horo domin cin dungumin ‘yan Boko haram. Rundunar sojin Nigeria tace soja sun kashe dandazon ‘yan tsagerar dake dauke da makamai, an kuma lalata mafi yawan dandalin da suke jan daga. Amma wani abin bakin cikin shine ganin yadda ake ci gaba da kaiwa farar hula hare-haren ta’addancin