Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Sake Kafa Dokar Hana Fita A Jihar Adamawa


Rundunar sojin Adamawa
Rundunar sojin Adamawa

Ranar Litinin da kungiyar Boko Haram ta kai wani mummunan hari kan sansanonin jami'an tsaro gwamnatin Borno ta kafa dokar hana fita to amma ta sassauta yanzu. Sai kuma gashi rundunar sojojin dake Adamawa ta kafa dokar hana fita. To ko menene dalilin yin hakan?

Yayin da gwamnatin jihar Borno ke sassauta dokar hana fita da ta kafa biyo bayan harin da kungiyar Boko Haram ta kai kan sassanonin jami'an tsaro a Maiduguri ranar Litinin, sai gashi sojojin dake jihar Adamawa sun kafa dokar hana fita a jihar lamarin da ya baiwa kowa mamaki.

Rundunar Soji na 23 dake garin Yola jihar Adamawa ta sake kafa dokar hana fita a garuruwan Mubi ta Arewa da Mubi ta Kudu tun daga karfe bakwai na marece har zuwa biyar na safe a wani matakin da ta kira na yaki da masu tayar da kayar baya. To sai dai ba kaman jihohin Borno da Yobe ba inda gwamnoni ne ke kafa dokar hana fita, a jihar Adamawa wadda ke cikin dokar ta baci kamar Borno da Yobe, sojoji ne ke kafa dokar ta baci.

Sanarwar kafa dokar da ta samu sa hannun Kaftein M. A. Umar ta ce kananan hukumomi biyu ne kawai dokar ta shafa yayin da sauran kananan hukumomin zasu cigaba da yadda aka saba tun farko wato daga karfe goma sha daya na dare har zuwa karfe biyar na assubahi. Wannan sabuwar dokar ta zo ne yayin da mutanen kananan hukumomin biyu ke kokawa dangane da yanke masu layoyin sadarwa da aka yi.

Mutanen yankin sun ce da suna samun damar fita su nemo abun da zasu ci to yanzu an hana su fita. Suna gani a kutunta masu an takure masu rayuwa domin babu fita kuma babu hanyar sadarwa. Sun koka suna son a sassauta masu. Sun ce ko mutanem Maiduguri da aka kai masu hari an dawo masu da layukan sadarwa. Don haka su ma ya kamata a dawo masu da nasu.

Masana harkar tsaro irin su Dr Abdullahi Bawa Wase gani suke ya kamata gwamnatin tarayya ta sake salo. Katse layuka da kakaba dokar ta baci ba su ne mafita ba. Ya ce shugabannin Najeriya ya kamata su yi la'akari da abubuwan dake faruwa a duniya. Misali Amurka ta yi shekara goma tana fafatawa da kungiyar Taliban a Afghanistan to amma daga wannan shekarar ta nemi yadda zata tattauna da kungiyar. A halin yanzu shugaban Afghanista Ahmed Karzai ya ki ya sa hannu a takardar yarjejeniyar tsaro da Amurka sai dai idan zasu soma tattaunawa da kungiyar Taliban, kungiyar da ake ganin ita ce abokiyar gaba. Ya ce a lura da Amurka ta shiga kasar tana zaton zata murkushe 'yan Taliban cikin dan lokaci kadan to amma gashi yau an kai shekara goma da wani abu. To idan haka a keyi a kasashen duniya a samu sulhu to shugaban Najeriya yakamata ya yi anfani da wannan. To sai dai wadanda suke anfana daga rigingimun zasu dinga juya mashi hankali su kaishi su baro har a haifi dan da bashi da ido a kasar.

Haka ma wani jami'in tsaro na farin kaya da ya yi ritaya yana ganin akwai bukatar kafin ta natsu wajen yaki da masu tada kayar baya. Ya ce dokar ta baci bata yi anfani ba sabili da haka ya kamata a samo wasu hanyoyin da za'a kawo karshen tashin hankali a kasar. Dokar ta baci ba zata magance matsalar da kasar ke ciki ba.

Ibrahim Abdulaziz nada rahoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Shiga Kai Tsaye

.
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG