WASHINGTON DC - Sanarwar daya fitar a yau Laraba, jami'in yada labaran rundunar wanzar da zaman lafiya ta Hadarin Daji a jihar Zamfara, Laftanar Suleiman Omale tace, dakarun sun nuna matukar jarumta da sadaukarwa yayin samamen, daya kai tarwatsa 'yan bindigar.
Da yake bayyana yadda samamen daya kai ga kubutar da mutanen da aka yi garkuwa dasun, yace dakarun sun samu kiran gaggawa a daren 12 ga watan Maris din da muke ciki, inda suka shiga musayar wuta tsakaninsu da 'yan bindigar sa'ilin da suka isa garin tsafe.
Saidai, ta hanyar amfani da mafificin salo da jajircewa, dakarun sun ce murkushe gungun 'yan bindigar, abinda ya tilasta musu arcewa da raunukan harsashi zuwa cikin dazuka da tsaunuka tare da barin mutane 10 da suka yi garkuwa dasu.
A yayin sintirin tsaftace yankin, zaratan dakarun sun yi nasarar kubutar da mutane 10 da aka yi garkuwa dasu tare da sadasu da iyalansu.
Sanarwar ta kara da cewar, babban hafsan dake kula da shiyar Sokoto, ya yaba da jajircewa, jarumta da kwarewar aiki da dakarun suka nuna inda ya jinjinawa kokarinsu tare da umartarsu dasu ci gaba aikin wanzar da zaman lafiya da tsaro a yankin.