Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yaran Najeriya Sun Cancanci Samun Ilimi Cikin Kwanciyar Hankali - UNICEF


Asusun Tallafawa Kananan Yara Na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) yayi Allawadai da harin baya-bayan nan da aka kai kan wata makaranta a jihar kaduna.

A sanarwar daya fitar a yau Juma’a, wakilin UNICEF a Najeriya, Christian Munduate, ya bayyana takaici game da harin, inda yace yaran Najeriya sun cancanci samun ilimi a yanayi na lumana.

Wakilin asusun na UNICEF ya kara da cewar, kamata yayi makarantu su kasance killatattun wurare na neman ilmi da ci gaba amma ba bigirorin tsoro da tashin hankali ba.

An ruwaito sanarwar na cewa, “nayi matukar bakin ciki da damuwa game da wannan rahoto na sake sace dalibai a jihar Kaduna. Yawaitar irin wadannan al’amura a fadin Najeriya alama ce ta tashin hankalin dake bukatar daukar matakan gaggawa masu tsauri daga dukkanin matakan gwamnati da al’umma. Kamata yayi makarantu su zama kebabbun wuraren neman sani da ci gaban dan adam, amma ba bigirorin tsoro da tashin hankali ba”.

“Satar dalibai na baya-bayan nan, kamar wadanda suka gabace shi, abin allawadai ne kuma wani bangare ne na salon kai hare-hare akan cibiyoyin ilimi, musamman ma a shiyar arewa maso yammacin Najeriya, inda kungiyoyi ‘yan bindiga suka zafafa kai hare-hare da yin garkuwa da mutane. Kwana guda kafin afkuwar wannan lamari, jami’in Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya ya zanta akan satar dimbin mata da ‘yan mata harma samari da mayakan kungiyar Boko Haram suka yi a jihar Borno”.

“Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, da hadin gwiwar wasu jami’an Najeriya na taimakawa wajen kwantar da hankulan iyaye da dangin yaran da aka sace.

UNICEF ya dukufa wajen yin hadin gwiwa da gwamnatoci da al’umma da kungiyoyin bada agaji domin magance dalilan dake jefa yara cikin tashin hankali tare da bada kariya ga makarantu daga kowace irin barazana da tashin hankali.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG