ANAMBRA, NIGERIA - Rahotanni sun ce limamin cocin yana jan ragamar hidimar mujamia'r ne a lokacin da ‘yan bindigan suka afka wa cocin suka tarwatsa mabiya da harbe-harbe a iska kafin daga bisani suka yi awon gaba da shi.
A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Mista Daniel Ndukwe, “Jiya da misalin karfe hudu da kwata na yamma, da yunkurin ‘yan sanda da ‘yan sintiri da masu gadin daji wadanda suka kakkabe dajin da ake zargin an shiga da limamin cocin, ‘yan bindigan sun watsar da shi sun gudu. Kuma cikin ikon Allah an kubutar da shi lami lafiya.”
Daga karshe kakakin ‘yan sandan ya ce ce ana nan ana kara himma don zakulo masu garkuwar.
A yankin Nsukka dai ana murna ana barka don dawowar limamin cocin, in ji Reverend Fada Emmanuel Asadu, daraktan yada labarai na cocin Katolika a yankin.
Ya ce, “muna godiya ga Allah da ya dawo mana da shi lafiya. Ina tare da shi da wasu limaman coci yanzu, muna murna muna tattaunawa game da abin da ya faru.”
Jihar Enugu dai ba ta ji da dadi ba a karshen makon da ya wuce saboda halaka tsohon kwamishinan raya karkara Mista Gabriel Onuzuluike da wansa Elvis Onuzuluike, da wasu ‘yan sanda biyu da ‘yan bindiga suka yi, lamarin da na ci gaba da baza fargaba a fadin Jihar.
Saurari cikakken rahoto daga Alphonsus Okoroigwe:
Your browser doesn’t support HTML5