Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu ‘Yan Bindiga Sun Sace Limamin Katolika A Jihar Filato, Sun Bukaci Naira Miliyan 50


Wasu 'yan bindiga.
Wasu 'yan bindiga.

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da limamin cocin Katolika mai kula da cocin St Anthony’s Parish, a unguwar Angware ta karamar hukumar Jos ta Gabas a jihar Filato.

'Yan bindigan da suka yi garkuwar da limamin, Rev James Kantoma sun bukaci a biya su N50m kudin fansa.

Gidan Talabijin na Channels ya rawaito cewa an sace limamin ne a ranar Lahadi da daddare a gidansa da ke unguwar a lokacin da ‘yan bindigar suka mamaye yankin suka yi ta harbe-harbe, daga bisani kuma suka kama sauran zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Shugaban kungiyar kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen jihar Filato, Rev Father Polycarp Lubo, ya tabbatar da sace limamin cocin.

Ya ce wadanda suka yi garkuwa da su sun yi tuntuba kuma suna neman a biya su Naira miliyan 50 kafin a sako limamin cocin, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar CAN a karamar hukumar.

Har ila yau, a wannan rana ne kuma masu garkuwa da mutane sun kuma sake yin awon gaba da wani Bishop na Anglican, Reverend Oluwaseun Aderogba na Jebba Diocese, jihar Kwara, da matarsa, da direban motar.

An yi garkuwa da su ne a sabuwar hanyar Oyo/Ogbomoso a jihar Oyo.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, Adewale Osifeso, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar.

Ya bayyana cewa wani Rabaran Adekunle Adeluwa ne ya kai rahoton faruwar lamarin a hedikwatar ‘yan sanda na Atiba.

A cewar Osifeso, binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa motar wadanda abin ya shafa ta sami wata matsala a lokacin da ta tashi daga Yewa a jihar Ogun zuwa Jebba a Kwara.

Kakakin ya bayyana cewa, an umurci mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da ayyuka na rundunar da ya dauki nauyin aikin da zai kai ga ceto wadanda lamarin ya shafa.

XS
SM
MD
LG