Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Garkuwa Da Wani Limamin Cocin Katolika A Arewacin Najeriya


BORNO: Taron limaman Darikar Katolika na Sojojin Najeriya.
BORNO: Taron limaman Darikar Katolika na Sojojin Najeriya.

An yi garkuwa da wani limamin cocin Najeriya daga gidansa da ke arewacin Jihar Kaduna a Najeriya, in ji wata sanarwa da kungiyar darikar Katolika ta fitar a ranar Talata, a karon farko da aka samu rahoton sace wani malamin addini a Jihar tun watan Yuli.

Kungiyoyin ‘yan bindiga dauke da makamai suna cin karensu ba babbbaka a arewacin kasar inda suke yin fashi ko yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, kuma ana ta samun tashe-tashen hankula, inda jami'an tsaro suka kasa dakile hare-haren.

Kungiyar ‘Yan Bindiga
Kungiyar ‘Yan Bindiga

Uba Christian Okewu Emmanuel, shugaban darikar Katolika na Kaduna, ya ce an sace Reverend Father Abraham Kunat, wani limamin coci a kauyen Idon Gida, a wani gida da yake zaune a wani gari, bayan ya bar cocin sa saboda rashin tsaro.

Ba a samu jin ta bakin kakakin ‘yan sandan Kaduna ba, domin jin nasu ra’ayin game da lamarin.

-Reuters

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG