Mahalarta taron da suka kunshi malaman addinin musulunci da shugabannin Majami’u, su kimanin 50 da suka fito daga cikin da wajen Kano, sunyi musayar ra’ayi da fasaha kan rawar da jagororin addinan ke takawa wajen magance matsalolin rashawa da cin hanci a dukkannin matakai, da kuma wanzar da shugabanci na gari.
Jakadan sakataren harkokin wajen Amurka na musamman akan lamuran hulda da musulman duniya Mr. Shaarik Zafar, wanda ya jagoranci taron ya bayyana gamsuwa game da bayanai da lafazin jagororin addinan.
Farfesa Haruna Wakili dake zaman daraktan cibiyar Manbayya masu karbar bakuncin taron, yace Manbayya cibiya ce ta komai da ruwanka in dai ana magana ne kan batun shugabanci na gari.
Saurari cikakken rahotan Mahmud Ibrahim Kwari daga Kano.
Your browser doesn’t support HTML5