Wani sojan Amurka ya rasa ransa, kana wasu hudu sun ji jikkata, bayan da mayaka masu alaka da Al Qaeda suka kai farmaki a wani matsugunin tsaro da ake kan ginawa a kudu maso yammacin Somalia.
Harin wanda aka kai ranar Juma’a, ya faru ne a arewa da birnin Kiyamo mai nisan kilomita 50, a daidai lokacin da dakarun Amurka ke taimakon takwarorin aikinsu na Somalia da Kenya, wajen gina matsugunin tsaron, a wani mataki na kakkabe yankin daga kungiyar Al Shabab, a cewar jami’an Amurka.
Wadanda suka shaida harin, sun ce lamarin ya faru ne a kusa da garin Sanguni, a daidai lokacin da dakarun Amurka da na Somalia suke tona wani rami da gina sauran matakan tsaro.
Sun kara da cewa, da farko, maharan sun ta-da bama-bamai, kafin daga baya su bude wuta akan dakarun na Amurka da na Somalia.
Amurka ta ce an jikkata wani sojan Somalia guda, amma shaidu sun ce an kashe har da dakarun na Somalia.
Tuni dai kungiyar ta Al Shabab ta dauki alhakin kai wannan hari ta kafar yada labaranta ta “Shahada News Agency.”