Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Maida 'Yan Ciranin Kasar Somaliya sama da Gida


Wadansu 'yan ci rani a tekun baharan
Wadansu 'yan ci rani a tekun baharan

Hukumar kula da ‘yan ci rani ta kasa da kasa (IOM) tace, ta maida ‘yan ci ranin kasar Somaliya dari da hamsin da suka makale a kasar Libya cikin makon da ya gabata. Galibi an tsare su a cibiyoyin da gwamnati take tsare ‘yan ci rani na tsawon watanni a cikin mummunan yanayi.

Hukumar ta hakikanta cewa, akwai kimanin mutane miliyan daya, galibi daga kasashen larabawa da kasashen nahiyar Afrika da suka yi tafiya mai hadarin gaske zuwa Libya da nufin shiga kasashen turai domin samun ingancin rayuwa.

Sai dai, a zahiri idan suka isa kasashen sai suga ba haka lamarin yake ba. Hukumar ta IOM tace ‘yan ci ranin dake Libya suna fuskantar hadura da dama da suka hada da fasa kwauri da safarar bil’adama, da garkuwa da mutane, da kunci, da tsarewa, da kuma gasa masu akuba. Kakakin hukumar Joel Millman yace shirin hukumar dake ba masu sha’awar damar komawa gida, ya maida dubban ‘yan ci rani daga kasashe dabam dabam gida.

Millman yace “Mun hakikanta cewa jiragen saman da hukumar IOM take tanadawa da kuma ayyukan da take gudanarwa a Libya, suna taimakawa wajen maida mutane gida, kuma suna rage hadarin da ‘yan ci rani dake tsallake tekun baharum suke fuskanta.”

Alkaluma sun nuna cewa kimanin ‘yan ci rani da ‘yan gudun hijira daga kasar Somaliya dubu talatin ne suka fice daga Libya, ta cikin teku zuwa kasar Italiya tun shekara ta dubu da dari biyu da goma sha hudu.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG