Kasar Habasha ta ba da sanarwa jiya Talata cewa za ta mika ma kasar Eritea wani yankin kasa da su ka jima su na takaddama akai.
Kwamitin Gudanarwar gamayyar jam'iyyun da ke mulkin Habasha (EPRDF, a takaice), ta ce za ta mutunta yarjajjeniyar da aka cimma a Algiers, wadda ta haifar da shawarar da aka yanke game da kan iyakar Habashar da Eritrea. Kasashen duniya sun amince da yarjajjeniyar, wadda aka rattaba ma hannu a 2002, kuma su ma bangarorin biyu sun amince da sharuddan da Kwamitin Shata Kan Iyaka na Majalisar Dinkin Duniya, MDD ya gindaya.
To amma kasar Habasha ta hana a shata kan iyakar, wanda hakan ya haddasa tashin hankalin da aka kasa warwarewa, da kuma fito na fito na tsawon shekara 16 a tsakanin kasashen na gabashin Afirka makwabtan juna.
Kwamitin na EPRDF ya ce shawarar da ya yanke jiya Talata ta biyo bayan nazarin matsalar tsakanin Habasha da Eritrea da kuma sha'awar tabbatar da zaman lafiya tsakanin al'ummomin kasashen biyu.
Yarjajjeniyar ta Algiers, wadda aka rattaba ma hannu a 2000, ta biyo bayan shafe lokaci mai tsawo da aka yi ana ta gwabza mummunan yaki tsakanin Habasha da Eritrea. Bayan da yakin ya zo karshe, Kwamitin Shata Kan Iyaka ya kwashe shekara da shekaru ya na kokarin shata kan iyaka tsakanin kasashen biyu. An yanke shawarar ce bisa ga ikirarin kowacce daga cikin kasashen biyu da kuma taswirar zamanin mulkin mallaka na 1900s.
Facebook Forum