Yan kasuwa daga kasashe makwabtan Kamaru da Gabon suna shiga da kaya kuma suna fita da wasu daga karamar kasar ta tsakiyar Afrika. Ephraim Mukwah mai shekaru 43 dan Kamaru matukin motar daukar kaya, yace suna murna cewa a karshe jami'an Equatorial Guinea sun basu daman shiga Kamaru
Ya ce mutane sun yaba kuma sun yi murna, yayin da aikin taxi yake bunkasa a cikin garin kana motocin daukar kaya da kiya-kiya zasu iya zurga-zurga har zuwa Bata babban birnin kasar dake kan iyakar kasar da Kamaru ba tare da wata damuwa ba.
Ana samun daman kai kayan abinci daga Kamaru na kayan gini da na motoci zuwa Equatorial Guinea, yayin da ita Equatorial Guinea din take kai abubuwan sha da man girki zuwa Kamaru.
Facebook Forum