An Kashe Mutane 22 A Wani Hari Da Aka Kai A Yammacin Nijar

Yan bindiga a yankin Tillaberi 

Wasu da ake zargin mayakan IS ne sun kashe mutane 22 a hari da suka kai a wani kauye da ke yammacin Jamhuriyar Nijar  kusa da kan iyaka da Mali, kamar yadda wasu majiyoyi na cikin gida suka shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa a ranar Litinin.

Harin na ranar Lahadi ya faru ne a kauyen Motogatta da ke yankin Tillaberi inda Nijar ke iyaka da Mali da Burkina Faso, inda kungiyoyin masu da'awar jihadi suka kwashe shekaru suna gwagwarmaya.

“Mutane 22 ne suka mutu a harin, ciki har da wasu ‘yan banga,” in ji wani zababben jami’in yankin.

Wani mazaunin garin da ke kusa ya tabbatar da faruwar lamarin.

Jami’in ya ce maharan sun isa kauyen ne a kan babura da misalin karfe 4 na yamma.

"Sun fara harbe-harbe, inda suka kashe mutane nan take," in ji shi.

Kasar Nijar dai na fama da tashe-tashen hankula biyu na, da na 'yan kungiyar IS wanda ya mamaye kudu maso gabashinta daga yakin da aka dade ana fama da shi a makwabciyarta Najeriya, da kuma farmakin da 'yan bindiga suka tsallaka daga Mali da Burkina Faso a yammacin kasar.

A lokacin da shugabannin sojoji suka hambarar da zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli, sun bayar da hujjar tabarbarewar harkokin tsaro a kasar ne.

A ranar 17 ga watan Disamba, jagoran juyin mulkin Janar Abdourahamane Tiani ya ce al'amuran tsaro na ci gaba da daidaituwa bayan da sojojin suka samu nasarori da dama wajen kwantar da tarzoma.