Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutane 52 A Wani Yanki Wanda Ya Hada Sudan Da Sudan Ta Kudu


SSUDAN
SSUDAN

Fiye da mutane 50, da suka hada da mata da kananan yara ne aka kashe a hare-haren da aka kai kan iyakar Sudan ta Kudu da Sudan, in ji wani jami’in yankin a ranar Litinin, a wani lamari mafi muni a hare-haren da ake kaiwa tun shekarar 2021 mai alaka da rikicin kan iyaka.

WASHINGTON, D. C. - Ministan Yada Labarai na Yankin Abyei, Bulis Koch, ya zargi matasa daga jihar Warrap ta Sudan ta Kudu da kai farmakin a yankin Abyei mai makwabtaka da su.

Yankin Abyei na da arzikin man fetur da ke karkashin hadin gwiwar Sudan ta Kudu da Sudan, wadanda dukkansu ke neman mallaka.

Koch ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa mutane 52 da suka hada da mata da yara da jami'an 'yan sanda ne aka kashe a hare-haren na ranar Asabar. Wasu 64 kuma suka jikkata.

“Saboda mawuyacin halin tsaro da ake ciki a yanzu, wanda ya haifar da fargaba da firgici, mun sanya dokar hana fita,” inji shi.

A ranar Lahadin da ta gabata ne Rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Abyei (UNISFA) ta bayyana cewa an kashe wani ‘dan kasar Ghana mai aikin wanzar da zaman lafiya na dakarun Majalisar Dinkin Duniya dake Abyei a lokacin da aka kai hari a sansaninsu da ke garin Agok a lokacin tashin hankalin.

Koch ya ce daruruwan fararen hula da suka rasa matsugunansu sun nemi mafaka a sansanin UNISFA.

William Wol, Ministan yada labaran jihar Warrap, ya ce gwamnatinsa za ta gudanar da bincike tare da gwamnatin Abyei.

An dai sha samun tashe-tashen hankula a yankin Abyei tsakanin gungun 'yan kabilar Dinka da ke gaba da juna da ke da alaka da inda aka ware kan iyakokin kasar da ke zama tushen samun kudaden haraji.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG