An Kashe Mutane 15 A Sabon Rikici Da Ya Barke A Wani Yankin Sudan Ta Kudu

Wasu mayakan Sudan

Wasu matasa sun harbe har lahira mutane 15 a yankin gabashin Pibor na kasar Sudan ta Kudu, ciki har da wani kwamishinan lardin, kamar yadda wani babban jami'i ya bayyana a ranar Laraba, a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula a yankin gabanin zaben kasar a karshen shekara

WASHINGTON, D. C. - Yakin basasa dai da ya barke tun shekaru biyu bayan da kasar ta samu 'yancin kai daga Sudan ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tsakanin shekarar 2013 zuwa 2018.

An dai samu zaman lafiya tsakanin manyan 'yan ta'adda tun daga wancan lokacin, amma ana ci gaba da gwabza fada tsakanin kungiyoyin masu dauke da makamai.

Wasu masu fafutuka sun ce sun yi imanin karuwar kashe-kashen na baya-bayan nan na da alaka da kuri’ar da za ta zabi shugabannin da za su gaji gwamnatin rikon kwarya ne a yanzu.

Harbin ya faru ne a ranar Talata lokacin da kwamishinan gundumar Boma da ke Pibor ke dawowa daga ziyarar da ya kai wani kauye.

"Kwamishinan da tawagarsa sun je kauyen Nyat kuma bayan dawowar sa an yi masa kwanton bauna inda aka kashe mutane 15, ciki har da kwamishinan," Abraham Kelang, Ministan yada labarai na yankin Greater Pibor ne ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Daga cikin wadanda suka mutu akwai mataimakin kwamandan sojojin Boma, jami'an gwamnati da kuma masu gadin kwamishinan lardin, in ji Kelang. Ya ce maharan na zargin matasan kabilar Anyuak ne na yankin.

An kuma zarge su da laifin kashe wani kwamishinan karamar hukumar Pibor da wani jami'in tsaro a bara. Jami'ai daga gundumar Pochalla, inda 'yan kabilar Ayuak din suka fi yawa, ba a samesu ba domin yin karin bayani ba.

Sudan

Gundumar Boma wadda galibi ta kabilar Murle ne ke da zama, ta sha fama da tashe-tashen hankula a lokaci-lokaci tsakanin kabilar Murle da Anyuak da kuma wasu kabilu daga jihar Jonglei mai makwabtaka. Wasu daga cikin tashe-tashen hankula na faruwa ne sakamakon satar shanu.

Sama da mutane 150 ne aka kashe a karshen watan Janairu da farkon watan Fabrairu a arewaci da yammacin Sudan ta Kudu a rikicin da ake yi tsakanin kungiyoyin da ke gaba da juna.

A ranar Talata ne Amurka, Birtaniya da Norway suka yi kira ga shugabannin Sudan ta Kudu da su dauki matakan gaggawa don tabbatar da zaben da za a yi na gaskiya kuma cikin lumana.

-Reuters