Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikici Tsakanin Makiyayan Sudan Ta Kudu Ya Kashe Mutane Akalla 39


Wasu Makiyaya
Wasu Makiyaya

Akalla mutane 39 suka mutu a fada da ta barke tsakanin makiyaya daga jihohi biyu da ke makwabtaka a Sudan ta Kudu,in ji jami'ai, inda suka dora alhakin rikicin kan filaye da aka dade ana yi.

WASHINGTON, D. C. - Sudan ta Kudu dai na fama da matsalar rashin tsaro tun bayan samun ‘yancin kai daga Sudan a shekara ta 2011. Yarjejeniyar zaman lafiya da ta kawo karshen yakin basasa tsakanin shekara ta 2013-2018 ta yi matukar rage tashin hankali, amma ana yawan samun ‘yan tashe-tashen hankula tsakanin al’ummomin da ke gaba da juna.

Ana ci gaba da samun tashe-tashen hankula ne a yankunan da ake takaddama kan hakkokin wuraren kiwo, ruwa, filayen noma da sauran albarkatu.

A makon da ya gabata, an kashe mutane sama da 50 da suka hada da mata da yara da kuma dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya biyu a kan iyakar Sudan ta Kudu da Sudan a lokacin da mazauna wani yanki suka kai hari kan wadanda suka fito daga wani bangare na rikicin kan iyaka.

A wani lamari na baya-bayan nan dai an gwabza fada tsakanin makiyaya a garuruwan Lakes State da Warrap tun a ranar Larabar da ta gabata, ya kuma ci gaba da faruwa har zuwa ranar Alhamis.

Hakazalika, a jihar Lake an ruwaito inji kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Manjo Elijah Mabor Makuach na tabattar da mutuwar mutane 20 sannan wasu 36 suka jikkata,.

A jihar Warrap makwabciyarta kuma an kashe mutane 19 tare da jikkata 17, in ji William Wol, ministan yada labaranta.

Makuach ya ce jami'an tsaron Lakes States da aka tura wurin da rikicin ya faru sun dakile tashin hankalin.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG