WASHINGTON, D. C. - Peter Biar Ajak ya gudu zuwa Amurka ne tare da taimakon gwamnatin Amurka shekaru hudu da suka gabata bayan da ya ce shugaban Sudan ta Kudu ya ba da umarnin a sace shi ko kuma a kashe shi. An bayar da biza cikin gaggawa wa Ajak, mai shekaru 40 a lokacin, da iyalansa bayan sun shafe makonni suna buya a Kenya. A yanzu yana zaune ne a jihar Maryland.
Wani korafin da gwamnatin tarayya ta yi a ranar Litinin a jihar Arizona ta tuhumi Ajak da wani Abraham Chol Keech mai shekaru 44, na Utah, da hada baki wajen saye da fitar da makamai ba bisa ka'ida ba ta hanyar wata kasa kuma zuwa Sudan ta Kudu. Tarin makamai wanda ya saba wa dokar hana fitar da makamai da kuma hana fitar da kayayyaki, wato Arms Export Control Act da Export Control Reform Act.
Makaman da aka yi la’akari da su sun hada da bindigogi masu sarrafa kansu kamar AK-47, na’urorin harba gurneti, na’urorin makami mai linzami na Stinger, gurnetin hannu, bindigogin maharba, albarusai, da sauran makaman da ake sarrafa su zuwa kasashen waje.
Duk da cewa jami’an shari’a ne suka bayyana korafin laifin, har yanzu ba a samu karar a tsarin intanet na gwamnatin tarayya ba a yammacin ranar Talata. Don haka ba a sani ba ko mutanen suna da lauyoyin da za su iya magana kan tuhumar da ake musu.
"Kamar yadda ake zargi, wadanda ake tuhumar sun nemi shigar da manyan makamai da albarusai daga Amurka ba bisa ka'ida ba zuwa Sudan ta Kudu, kasar da Majalisar Dinkin Duniya ta sanya wa takunkumi saboda tashin hankalin da ke tsakanin kungiyoyin da ke dauke da makamai, wanda ya yi sanadin kashe dubban mutane da kuma rabasu da muhallansu," in ji Mataimakin Atoni Janar Matthew G. Olsen na sashen tsaro na ma'aikatar shari'a; ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa.
Gary Restaino, lauyan Amurka na Arizona ya ce "Takunkumi da sarrafa fitar da kayayyaki na taimakawa ne wajen tabbatar da cewa ba a yi amfani da makaman Amurka a duniya ba don wargaza sauran kasashe masu ikon kansu."
Wani mutum wanda ya amsa wayar tarho a ranar Talata a ofishin jakadancin Sudan ta Kudu da ke gundumar Washington ya ce tawagar ba ta da jami’in yada labarai kuma jakadan ya yi tafiya ne saboda haka ba zai samu zarafin amsa tambayoyi kan lamarin ba.
-AP
Dandalin Mu Tattauna