Wannan bom dai ya fashene a wata cibiyar bankin First Bank, a lokacin da jama’a suka taru domin karbar kudade.
Wasu shaidun gani da ido, sun shaidawa Muryar Amurka cewa mutane 7 ne suka rasa rayukansu, sannan akwai wasu mutane 15 sun samu raunuka, kuma an garzaya da su asibiti.
Fashewar bom din keda wuya, jama’a suka kai dauki inda abun ya faru.
Ya zuwa yanzu babu wanda ya fito yayi ikirarin kai wannan hari, kuma babu wanda ya bayyana wani ko wata kungiya da ake zargi da kai wannan mummunan hari. Sai dai shaidun gani da ido, sunce suna kyautata zaton anyi amfani da babur ne wajen kai harin, saboda kasancewar baraguzen babur mai ci da wuta a kusa da bankin.
A halin yanzu dai, jami’ai sun bayyana cewa mutane 14 ne suka rasa rayukansu, wadanda suka samu raunuka kuma sun kai 40.
Your browser doesn’t support HTML5