Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Gudun Boko Haram a Kano


Jama'an da suka kauracewa gidajensu biyo bayan harin 'yan Boko Haram, sun samu mafaka a wata Makaranta, a Maiduguri, 2 ga Satumba 2014.
Jama'an da suka kauracewa gidajensu biyo bayan harin 'yan Boko Haram, sun samu mafaka a wata Makaranta, a Maiduguri, 2 ga Satumba 2014.

Yanzu haka kimanin ‘yan gudun hijira kimanin dubu biyu ne ke neman mafaka a kano sannadiyyar rikicin Boko Haram a jihohin Borno da Yobe da Adamawa baya ga wadanda rikicin kabilanci a jihar Taraba ya tilasta su kauracewa gidajen su.

Kaltuma daga Michika tace “Boko Haram ne suka kore mu. Bindiga, suna ta kashe jama’a, shine mu kuma muka tsorata, muka gudu. Bamu da kowa anan, bamu san kowa ba.”

Alhaji Muhammadu daga Michika yace “mun tafi Digil, sai aka ce mana ai Mubi ma tana gudu, da daddare sai muka ga mutane suna ta gudu daga Mubi ma.”

Hadiza daga Mubi tace “mun taso daga Mubi ne, sai aka zubar damu a daji, da kafa muka taka. Sai da muka samu motar Dangote, itace ta kawo mu nan Kano”.

Alhaji Bashir Aliyu, shine Sakataren zartaswa na Hukumar Bada Agajin Gaggawa a Jihar Kano.

“Gwamnati, ta bada kayayyakin agaji na abinci, da shimfida, da kayan girki duk muna raba musu”, inji Mr. Aliyu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG