Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bom Ya Fashe a Azare


A daren Laraba ne a garin Azare dake cikin Jihar Bauchi, wasu boma-bomai da aka daura akan babura suka fashe.

A daren Laraba ne a garin Azare dake cikin Jihar Bauchi, wasu boma-bomai da aka daura akan babura suka fashe, har suka sanadiyar rayukan a kalla mutane 8 da jikkata wasu. Wakilinmu Abdulwahab Muhammed yayi hira da wasu wadanda suka ga abunda ya faru.

Wani mazauni yace “walLahi wajen karfe tara da rabi, da babur, suka je bakin tasha ta kofar da ake fita, anan suka saka bom din, kuma babu wanda ya ga sanda bom din zai tashi. Yanzu mutane sun kai mutum 8 wadanda suka rasu.”

Mazaunin ya kara da cewa “har yanzu da nake magana, babu wani wanda ya ga mutanen da suka saka wannan bom.”

Hukumar ‘Yan Sandar Jihar Bauci ta aikawa ‘yan jarida da rubutaccen bayani dake dauke da sanya hannun kakakinta D.S.P Haruna Muhammed inda ta tabbatar da faruwar lamarin, amma tace mutane 5 suka rasa rayukansu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG