Masu ayyukan ceto a Taiwan, sun ce sun kammala kwashe dukkanin mutanen da bala’in girgizar kasa ta rutsa da su.
WASHINGTON D.C. —
A jiya Asabar aka kammala kwakulo gawarwakin wadanda wani ginin bene mai hawa 17 ya rufta akansu a birnin Tainan mai yawan mutane miliyan biyu.
Jami’an kasar sun ce adadin mutanen da suka mutu ya kai 116, bayan da girgizar kasar mai karfin maki 6.4 ta abkawa garin.
Mafi yawan wadanda suka mutu a cikin wannan bene ne da ke yankin Wei-guan.
Yanzu haka wanda ya gina benen da wasu mutane biyu na hanun hukuma bisa zargin cewa ba su bi ka’idojin da aka shimfida ba wajen yin ginin, lamarin da ya haddasa rugujewar gidan tare da kashe wasu mutanen da ke ciki.
Shi dai birnin na Tainan ya kasance yanki ne mai cike da masana’antu da kamfanoni.