Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A kasar Jamus wasu jiragen kasa sun ci karo da juna


Ma'aikatan ceto a wurin da jiragen suka ci karo
Ma'aikatan ceto a wurin da jiragen suka ci karo

Taho mu gama da wasu jiragen kasa suka yi a Jamus ya halaka rayuka da dama kana wasu suka jikata

‘Yansandan kasar Jamus sunce akalla mutane 9 ne suka hallaka, wasu sama da 100 suka sami raunukka a sanadin wani zo-mu-gama da wasu manyan jiragen kasa guda biyu suka yi a kasar.

Kampanin jiragen kasa na “Meridian” ya tabattarda cewa duka jiragen biyu nasa ne, suka gwabza tsakanin garuruwan Kolbermoor da Bad Abling wanda tazarar km 60 ta raba shi da birnin Munich.

‘Yansandan Jamus din sunce 50 daga cikin wanda suka ji rauni, raunin nasu mai tsananin gaske ne.

Har zuwa yanzu ba’a san mizanin yawan gudun da jiragen ke yi ba a lokacinda hatsarin ya auku.

Rescue personnel wait in Bad Aibling, Germany after two regional trains crashed, killing at least two people, Feb. 9, 2016.
Rescue personnel wait in Bad Aibling, Germany after two regional trains crashed, killing at least two people, Feb. 9, 2016.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG