Kasar Koriya ta kudu ta ce za ta dakatar da ayyuka a wani shirin hadin gwiwa da ta ke gudanarwa tare da makwabciyarta ta arewa a wata ma’aikata, wato a matsayin wani mataki na nuna fushinta bayan da arewar ta yi gwajin wani makamin roka.
Ministan hadin kan kasashen biyu Hong Yong- Pyo, ya gayawa manema labarai a yau Laraba cewa hukumomin Seoul na daukan matakan kare Pyongyong daga yin amfani da albarkatun da ta ke samu a wannan ma’aikata wajen samar da kudaden hada makamshin nukiliyanta.
“Da ya ke mun lura cewa wannan lamari baya canjawa, hakan ba kuma yana nufin za mu ci gaba da hulda ba, sai dai hakan na nufin aikin makamashin nukiliyan Korea ta arewa na ci gaba, wanda zai kai ga mummunan yanayi”
Ministan ya kara da cewa tuni an sanar da korea ta arewa game da dakatar da ayyuka a wannan ma’aikata.