Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taiwan: Ana Neman Wadanda Suka Tsira Bayan Girgizar Kasa


Masu ayyukan ceto na binciken baragizai domin neman wadanda suka tsira da rayukansu
Masu ayyukan ceto na binciken baragizai domin neman wadanda suka tsira da rayukansu

Dubban masu aikin ceto na can a kasar Taiwan suna kokarin kawar da gine-gine da suka rufe mutane bayan wata girgizar kasa da ta abkawa birnin Tainan a jiya Asabar, domin ganin ko za a samu wadanda suka tsira da ransu.

Ya zuwa yanzu hukumomi sun ce girgizar kasar mai karfin maki 6.4 ta halaka mutane 24, yayin da ta jikkata fiye da 500, a birnin na Tainan mai yawan mutane miliyan biyu.

Mafi yawan wadanda hadarin ya rutsa da su sun kasance ne a wani bene mai hawa 17, wanda ya ruguje baki daya.

Hukumomi sun ce za su yi bincike su ga ko an bi ka’idojin da aka shimfida wajen gina benen.

Ana dai hasashen akalla mutane 250 ke cikin dakunansu a lokacin da hadarin ya auku, inda yanzu haka ake kiyasin fiye da mutane 120 na makale a cikin baragizan gine-ginen.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG