Majalisar Dinkin Duniya ta haramtawa Korea ta Arewa amfani da fasahar makami mai linzami.
Da sanyin safiyar yau Korean ta yi gwajin a tashar Tongchang-ri da ke kusa da arewa maso yammacin kan iyakar kasar China.
Makamin dai ya nausa ne zuwa kudu maso yammaci, inda ya ketara ta saman tsibirin Okinawa da ke kasar Japan.
Daga baya Korean ta fitar da wata sanarwa ta kamfanin dillancin labaran kasarta, inda ta tabbatar da harba makamin rokan.
Wata rundunar sojin Amurka ta musamman ta ce ta ga gilmawar wani makami mai linzami a sararin samaniya, wanda ta ce an yi nasarar harba shi.
China da ta yi nuni da cewa wannan gwajin makamin ka iya zafafa zaman dardar din da ake ke yi a yankin.