An Kama Wasu Yara Kanana da Bom

An kama wasu yara kanana da bom, a Yola fadar Gwamnatin jihar Adamawa, da wasu da ba’a san ko su wanene ba suka basu da niyar kaiwa wani wuri dake kusa da barikin sojoji, a Yola.
Wannan dai na zuwa ne yayin da ake samun yawaitar kunar bakin wake, da akasari akan yi amfani ne da kananan yara.

Kamar yadda bayanai ke nunawa yaran ‘yan kimanin shekaru goma sha daya ne, sai da maimakon su kai inda aka turasu sai suka nufi wajen wani dan gwangwan da nufin saida masa.

Suna bari wajensa bada jumawa ba sai abun ya fashe inda ya raunata wasu jama’a.

Wani magidancin mai suna Umar DanKano, ya kalunalanci iyaye da yin sakaci akan ‘yayansu yana mai cewa komai talaucin Una yakamata ya lkai yaronsa makarata kuma ayi masu tarbiya na kin amsan kudi a hannun mutanen da bai sani ba.

Yawancin jama’a, sun farga sun fahimci cewar wadannan mutane muyagun ne sabida haka kowa ma gudunsu yake to kwai abun da ya rage masu shine sun din ka amfani da yara kanana wadanda basu san ciwon kansu ba.