Mutanen da ‘yan sanda suka samu nasarar kama sun hada da wani fitaccen dillalin bindigogi dan asalin Jamhuriyyar Nijar mai suna, Shehu Ali Kachalla, wanda ya ce ya shafe sama da shekara 3 yana kasuwancin makamai kamar yadda kafar yadda labarai ta Channels ta ruwaito.
Shehu Ali Kachalla, ya bayyana cewa, ya sayarwa ‘yan bindiga daban-daban akalla bindigogi 4, 500 a fadin yankunan arewa maso yamma a cikin shekarun da ya shafe yana wannan sana’ar ta shi ta sayar da makamai.
Sai wani dan bindiga mai suna Abubakar Ali, wanda ya bayyana cewa, yana gudanar da miyagun ayyukansa ne a tsakanin kananan hukumomin Kagarko da Chikun na jihar Kaduna.
Jami'in hulda da jama'a na 'yan sanda jihar ta Zamfara, Shehu Mohammed, ne ya bayyana hakan a yayin da ya ke gabatar da wadannan mutanen da ake zargi da aikata miyagun ayyukan a ranar Juma'a a shelkwatar rundunar dake birnin Gusau, fadar gwamnatin jihar.
Shehu Mohammed, ya ce an samu nasarar kama mutanen da ake zargin ne sakamakon hadin gwiwa tsakanin jami’an ‘yan sandan jihar da shugaban kungiyar makiyaya ta Miyyeti Allah wato MACBAN ta jihar Zamfara.
Ya kaa da cewa, rundunar ‘yan sandan jihar za ta ci gaba da hada gwiwa da duk kungiya ko mutanen da ke da ra’ayin taimakawa wajen samo zaman lafiya mai dorewa a jihar Zamfara da ma jihohin shiyyar arewa maso yamma baki daya.
Haka kuma, Shehu Mohammed ya bayyana cewa, rundunar ‘yan sandan jihar na aiki tukuru wajen tabbatar da cewa ta magance matsalolin tsaro gaba daya ta hanyar kawo karshen miyagun iri da suka addabi mutane don ganin jihar ta kubuta daga dukkan ayyukan ta'addanci.
Kayayyakin da aka kwato daga wadannan mutane da ake zargin, sun hada da bindigogi kirar AK-49 guda hudu, kirar magazines guda tara, albarusai guda 960, da layar tsubu ire-ire da dama.
Idan ana iya tunawa, jihohin arewa maso yamma musamman Zamfara, Katsina da Kaduna sun dade suna fama da ayyukan ‘yan bindiga dadi da ke addabar mutane, lamarin da ya kai ga asarar dumbin rayuka da dukikoyi.