Mukaddashin Sifeton ‘yan sandan Najeriya Usmana Baba, ya ba da umurnin a tura dumbin ‘yan sanda tare da daukan wasu matakai, don tabbatar da cikakken tsaro a duk fadin kasar gabanin bukukuwan Sallah.
Wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya Frank Mba ya fitar a ranar Laraba, ta ce wannan matakin kokari ne na daidaita al’amuran tsaron kasar, wadanda za su kare lafiyar al’uma.
“Shugaban ‘yan sandan Najeriya, ya fahimci cewa, akwai kalubale da ke addabar fannin tsaron kasar, amma ya ba da tabbacin cewa, wadannan kalubale ba su fi karfin rundunar ‘yan sandan ba.” Sanarwar ta ce.
Ya kara da cewa, matakan da aka dauka za su ci gaba da dorewa har zuwa bayan bukukuwan sallar.
Sanarwar ta kara da cewa, nan ba da jimawa ba, Najeriya, za ta shawo kan matsalolinta, inda shugaban ‘yan sandan ya jaddada cewa, rundunarsa “na kara himma wajen hada kai da sojojin kasar da sauran hukumomin tsaro, wajen tattara bayanan sirri.”
Sai dai shugaban ‘yan sandan, ya yi garagdi ga jami’ansa, da su yi aiki bisa kwarewa tare da nuna tausayi da tsari da kuma kare hakkin bil adama yayin gudanar da ayyukan nasu.