Shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriya, Farfesa Ibrahim Gambari ya ce barayi sun yi yunkurin shiga gidansa da safiyar ranar Litinin.
Kakakin shugaban kasa Garba Shehu ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter a ranar Litinin, yana mai cewa, barayin ba su yi nasarar kai wa ga cikin gidan ba.
“Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, ya tabbatar cewa, barayi sun yi yunkurin shiga gidansa da misalin karfe 3 na safe a yau (Litinin,) amma ba su yi nasara ba.” Garba Shehu ya ce, yana mai kwatanta yunkurin a matsayin na "rashin tunani."
Kakakin ya kara da cewa, “Farfesa Gambari wanda gidansa ke layin da ke gaba da na fadar shugaban kasa, ya bada tabbacin cewa, babu wani abin damuwa daga wannan lamari da ya faru.”
Karin bayani akan: Farfesa Ibrahim Gambari, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
A ‘yan kwanakin nan wasu unguwanni a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, na fuskantar matsalar tsaro, ciki har da ta masu yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa.
Rahotanni sun ce al’umomin wasu yankunan Bwari, Pegi da ke yankin Kuje da kuma Kubwa a birnin Abuja, sun kauracewa gidajensu saboda matsalar tsaro da ta addabe su.