Maganar matsalar tsaro dai ta kai mutukar da wasu ke ganin abun da ya rage wa al'uma shine addu'oin neman taimakon Allah wanda wannan ya sa masallacin Juma'a na NNPC dake Kaduna ya yi amfani da Azumin karshe a larabar Jjiya don addu'oin neman mafita game da matsalolin da ke damun Najeriya.
A hira da Muryar Amurka babban limamin masallachin Juma'an da ya jagoranci wadannan addu'oi Imam Zainil-abidin Usman ya bayana cewa makasudin wadannan addu'o'i ba wani abu bane ila matsalar da kasar baki daya ta ke ciki na tsaro.
Ya ce. "Ya kai wani mataki da ya gagari kowa amma kuma bai gagare ubangijinmu Allah SWA ba. Shi ya sa muka yi wannan taro domin kai kuka zuwa ga ubangijin mu game da kasarmu da kuma rokonsa ya kawo mana sauki musamman game da abun da ya shafi tsaro."
Wasu daga cikin malamai da masallatan da su ka halarci taron addu'oin sun ce babu wata addu'a illa addu'ar dai ita ce kawai mafita game da halin tsaro da ya addabi Najeriya.
Karin bayani akan: Allah, NNPC, Ramadan, Islama, Sallah, Muryar Amurka, Nigeria, da Najeriya.
Matsalar satar mutane don neman kudin fansa da afkawa garuruwa don kisan kiyashi dai na cikin manyan matsalolin da ke addabar kusan ko'ina a arewacin Najeriya duk kuwa da gwamnatin na cewa ta na iyaka kokarin kawo karshen wannan musiba baki daya.
Saurari cikakken rahoton a sauti: