Wani matashi dan shekaru 26 da ake zargi da kai wani mummunan hari da wuka a garin Solingen da ke yammacin kasar Jamus, ya shiga hannun 'yan sanda, kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka ruwaito a yammacin jiya Asabar, kimanin sa'o'i 24 bayan harin da ya hallaka mutane uku.
‘Yan sanda sun ki cewa komai nan take kan lamarin.
A baya kungiyar I.S ta dauki alhakin kai harin na wuka a ranar Juma'a wanda kuma ya raunata mutane takwas.
Tun da farko a jiya Asabar, 'yan sanda sun ce sun tsare wani matashi dan shekaru 15 da suka ce mai yiwuwa yana da alaka da harin amma suka ce ba’a kai ga kama wanda ya kitsa kai harin.
Daga bisani kuma 'yan sandan sun ce sun sake kama wani mutum na biyu a wani samame da suka kai wani gida na 'yan gudun hijira a Solingen.
'Yan sandan sun ce ba za su iya ba da karin bayani kan mutumin ko alakarsa da lamarin ba.
A yayin da ta ke bayyana mutumin da ya kai harin a matsayin sojan kungiyar IS, kungiyar mayakan ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Telegram cewa "ya kai harin ne domin ramuwar gayya kan abin da ake yi wa musulmin Falasdinu da sauran wurare."