Jami’an yankin sunce mayakan hudu sun tada bamabama da aka hada a cikin gida jiya Laraba, wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutum guda da kuma raunata mutane uku , bisa ga rahoton kafannin dillancin labarai na na gwamnati- Xinjhua . Rahoton yace, 'Yan sanda sun harbe maharan guda hudu , yayinda suka bayyana lamarin a matsayin harin ta’addanci.
An kashe daruruwan mutane a iyakar yankin Xinjiang a yan shekarun nan sakamakon mummunan tashin hankalin tsakanin musulman Uighur da kuma Yan kabilar Han na Sin, masu rinjaye.
Gwamnati ta dora alhakin tashin hankalin kan al'ummar Uighur masu tsatsa-tauran ra'ayi, wadanda ke neman yancin ci gashin kansu daga China. Sai dai kungiyoyin rajin kare hakin bil'adama da kuma Yan gudun hijira, suna masu ra'ayoyin cewa, Matsin lamba da kuma danniyar da gwamnati take yiwa addinin kailar Uighur da kuma al'adunsu ya haifar da tashin hankalin, zargin da gwamnatin China ta musanta.