Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fidda Sharuddan Yarjejeniyar Zaman Lafiya Tsakanin Israila Da Falasdinu


A jiya laraba,Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya fidda sharuddan da aka iya anfani dasu wajen samar da yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin Izraila da Falasdinu, sai dai kuma yayi gargadin cewa, kokarin da ake na ganin an sami kahuwar kasashen guda biyu a matsayin maganin matsalar, abu ne dake kara fuskantar babban cikas.

A cikin jawabin da Kerry yayi na tsawon sa’a guda a maaikatar na kasashen waje, Kerry ya kare matakin da Amurka ta dauka na kauracewa jefa kuri’a a zauren Majalisar Dinkin Duniya, lokacin taron kwamitin sulhu da ya la’anci Izraila saboda ci gaba da ginawa Yahudawa ‘yan kaka gida gidaje a yankunan Falesdinawa.

Dama dai kuriaar da aka jefa a Majalisar Dinkin Duniya, an jefa shi ne da zummar kare manufar samarda kasashe biyu makwaptan juna, inji Kerry wanda yayi fatali da sukan da akeyi wa Amurka na cewa wai ta tozarta babbar ýar gaban goshinta, wato Izraila.

Kerry yace wannan matsayar da Amurka ta dauka itace take a kanta har yanzu, watau ganin Izraila ta ci gaba da zaman kasar Yahudawa mai bin akidojin demokradiya.

Sakatare Kerry ya bayyana cewa kuriaar da aka jefa tayi dai-dai da manufofin Amurka.

Sai dai ba wani sabon kudiri da aka kara a cikin abubuwa shiddan da Kerry ya tabo a cikin jawabin sa, sai dai maimakon hakan jawabin sa ya jaddada mayar da hankali ne akan batutuwan da aka cimma matsaya akan su, watau maganar samun kasashen biyu (na Isra’ila da Palesdinu), wanda kuma itace manufar aksarin gwamnatocin Amurka da suka gabata.

XS
SM
MD
LG