Rahotannin dake fitowa daga Ankara babban birnin kasar Turkiyya sun ce Turkliyya da kasar Rasha sun cimma yarjejeniyar tsaida yakin a daukacin dukkan kasar Syria baki dayanta, to sai dai kasar ta Rasha taki tace uffan game da wannan batu haka suma ‘yan tawaye sunce ba wata matsaya da aka cimmawa game da wannan batu a hukumance.
Sai dai an jiwo Ministan harkokin wajen Turkiyyan Mevlut Cavusoglu na cewa akwai yarjejeniyoyi biyu da aka shata dangane da wannan lamarin na Syria, daya shine matsaya sulhun siyasa, na biyu kuma shine tsagaita wuta, kuma duka matakan biyu ana iya aiwatar da su a kowanne lokaci.