Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ta'addanci Da Mata Ke Aikatawa A Kasar Kenya Na Karuwa


A cikin watan satumbar data gabata wasu mutane ukku sun kaiwa caji ofis diin ‘yan sanda hari a Mombasa na kasar Kenya, inda suka daba wa daya daga cikin ‘yan sandan wuka kana suka banka wa caji ofis din wuta, kafin ayi nasarar harbe su har lahira. Kamar yadda majiyar ‘yan sanda take cewa.

Wannan lamari ya ja hankalin duniya ba wai don karfin wadanda suka kai harin ba a’a sai domin cewa wadanda suka aikata wannan danyen aikin dukan su ukkun mata ne.

Masana sun bayyana cewa ayyukan ta'addanci da mata ke aikatawa a kasar ta Kenya sai karuwa yake yi, suka ce sai dai wannan ba a Kenya kadai yake faruwa ba a’a har ma a nahiyar Africa abin ke shafa.

Suka ce wannan yasa kungiyoyin ‘yan taadda yanzu sai kara neman mutanen da zasu horas a cikin su, suke yi musammam wadanda suke ganin cewa ba a za a tuhume su ba, kuma zasu iya yawo a cikin birane da gitta shingen jamniaan tsaro ba tare da an bincike sub a, ba shakka wannan yana haifar da barazana kwarai da gaske.

Musali a arewa maso gabashin Najeriya da kuma kasar Kamaru , a tsakanin watan Juni na shjekarar 2014 da kuma watan Afirilu na shekarar 2016, jamiaan sun tantance mata 200 da suka jkai hari wanda yayi dalilin mutuwar mutane har dubu guda.

Phyllis Muema wadda take it ace babban darektan cibiyar kula da taimakon al’umma na kasar Kenya, kumna tana zaune ne a Mombasa, kuma tana aiki ne da matasa da kuma iyayen su dake da hadarin yiyuwar ‘yan taadda su shuka musu raayin su.

Muema tace ta lura a cikin ‘yan shekarun da suka gabata wadannan masiu raayin rikau sun mayar da hanksalin su wajen daukar mata su shiga cikin ayyukan taaddanci.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG